Matasa da malaman addinin musulunci da dama sun je coci don taya kiristoci shagalin bikin kirsimeti. Sannan sun kai wasu kyautuka na musamman don nuna yabawa a gare su.
Kamar yadda shugaban cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministary, fasto Yohanna Butu ya bayyana, duk shekara, daruruwan musulmai na taya su shagali zagayowar ranar haihuwar Jesus a cocinsa don kara kawo hadin kai.
KU KARANTA: Ƙungiyar kiristoci ta ƙara jaddada rashin amincewarta da takarar musulmai
Butu ya ce ‘yan Shi’a, ‘yan Tijjaniyya da Ahlul sunna duk suna zuwa cocin don taya su murnar. A cewarsa, sun je da kyautuka zuwa cocin don nuna soyayya, kauna, zaman lafiya da fahimtar juna.
Malamin ya ce duk da an yi wannan kirsimetin ana tsaka da rashin tsaro, talauci, tsadar rayuwa da rashin aiki, ana fatan dai komai ya saukaka.
Butu ya yi kira ga malaman addinai biyun da su kasance masu addu’a don ayi zabe cike da tsaro da zaman lafiya. Ya yi kira da a dinga yi wa jami’an tsaro addu’a don samun nasara a filin daga.
Ya bayyana cewa fiye da musulmai 1,000 ne suka je cocin tasu din taya su murna.
Ku Yi Koyi Da Kyawawan Dabi’un Annabi Muhammad— Shugaba Buhari Ga Al’ummar Musulmai
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su hada kai da gwamnati a kokarin da ake yi na kawar da matsalar tsaro da yaki da cin hanci da rashawa a kasar.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Shugaban ya yi wannan kiran ne a cikin sakonsa na fatan alheri ga al’ummar Musulmi a mauludin Mauludi na murnar zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W.