Wata matar aure ta bayyana wa duniya yadda ta yi lalata da direbanta kasancewar ta kwashe shekaru 6 da aure ba tare da samun juna biyu ba, Legit.ng ta ruwaito.
A cewa matar, babu yadda bata yi da mijin ba akan su je asibiti don a duba lafiyarsu amma ya ki amincewa, hakan yasa ta yanke shawarar tuntubar direbanta.
Ta ce yanzu haka yaransu biyu da direban, kuma abinda yasa ta sanar da duniya gaskiya batu shi ne kada nan gaba mijinta ya gane cewa ba yaransa bane.
Matar wacce asali ‘yar kasar Ghana ce ta bayyana wannan labarin nata ga TV3 Ghana inda ta ce har sau biyu direban nata ya dirka mata cikin kuma ta haifi yaran.
An sakaya bayanai dangane da matar inda tace ta yi shekaru 6 da aure, kuma babu kokarin da bata yi ba don ta samu ciki amma abin ya gagara.
Wannan lamarin yasa ta je har gaban likita don jin idan wata matsala ce ta same ta. Amma sai ya tabbatar mata da cewa lafiyarta kalau.
Amma a bangaren mijinta, ta ce ya ƙi zuwa asibitin don a duba lafiyarsa. Bayan ganin haka ne ta yanke shawarar samun mafita.
Ta bayyana direbanta a matsayin mutumin kirki wanda ta kulla kyakkyawar alaka da shi har ta kai ga sun fara kwanciya da juna.
A cewarta, garin hakan ne har ya dirka mata ciki na ɗaya, ta haihu, ya dawo yayi mata ciki na biyu, shi ma ta haihu.
Ta bayyana cewa direbanta ya san cewa yaran nasa ne. Amma mijinta bai farga da cewa ba nashi bane yaran.
Direba ya saci motar Uwargidansa, ƴan awanni bayan ya fara aiki
A ranar Laraba ne wata kotun majistare da ke Ikeja ta tsare Samuel Harrison a gidan yari na Kirikiri bisa zargin satar motar Ubangidansa da wasu kayayyaki masu daraja.
Alkaliyar kotun, Misis O. O Fajana ta bayar da umarnin tsare wanda ake kara bayan ya amsa laifin hada baki da sata.
Fajana ta dage sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Satumba domin yanke hukunci, kamar yadda NAN ta ruwaito.
Mutumin mai shekaru 46 da haihuwa yana zaune ne a unguwar Ilaje da ke Ajah a Legas.
Comments 1