Wani mutum ɗan ƙasar Ghana mazaunin ƙasar Jamus yayi bayanin yadda yanayin aikin sa na wanke-wanke yake kasancewa a rana.
Da yake tattaunawa da wani mai tashar Youtube, Zionfelix, Kofi Asiedu, ya bayyana cewa yana samun naira dubu ɗari takwas da saba’in (N870,000) kowane wata daga aikin nasa a ƙasar Jamus. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: NAHCON da Saudiyya sun sanya hannu kan yarjejeniyar aikin hajjin bana
Da yake kasafta yadda kuɗin suke, ƙaƙƙarfan ɗan ƙasar Ghanan wanda akayi hira da shi a wajen aikin sa yace yana samun €12 duk sa’a ɗaya sannan yana aiki ne a sa’o’i takwas a kwana biyar.
Sai dai ya bayyana cewa aikin wanke-wanke nada matuƙar wahala wanda yake buƙatar mayar da hankali da ƙwarewa.
A kalaman sa:
“Kaga zaka tsaya a tsaye kana aiki na tsawon sa’o’i takwas. Zaka hutu na minti goma zuwa ashirin ne kawai domin cin abinci.”
“A nan idan kana aiki baka yin wani abun daban kamar irin su hawa kafafen sada zumunta domin sanin abubuwan dake faruwa saboda maigidanka ba zai bari ba.”
Kofi Asiedu ya yarda da maganar da Zionfelix yayi, wanda ya shawarci ƴan’uwan ƴan ƙasar Ghana mazauna ƙasashen waje da kada su yi almubazzaranci da kuɗin da suke turo musu saboda suna ganin kamar a banza suke samun su.
Sojoji Sun Yi Ajalin Fitaccen Shugaban ‘Yan Bindiga Kachalla, Da Sauransu
A wani labarin na daban kuma, sojoji sun samu nasarar halaka wani ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga.
Kwanaki hudu bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar wa ‘yan Najeriya aniyar gwamnatinsa na karfafa nasarorin da aka samu a fannin tsaro, sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga da dama ciki har da Ibrahim Kachalla Gudau.
Gudau, wanda ya shahara kuma daya daga cikin manyan ‘yan fashi da makami, ya umurci wata kungiyar da ke yin garkuwa da mutane da kashe-kashe a Kafuna, Katsina, Zamfara da kuma wani bangare na Jamhuriyar Nijar.