Wani ƙayataccen bidiyo ya nuna wani matashi yana shan soyayya da wata kyakkyawar baturiya.
A cikin bidiyon wanda wani mai amfani da sunan @cyprianandsarah a manhajar TikTok ya sanya, matashin ya bayyana cewa ya haɗu da masoyiyar tasa ne a Instagram. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Bayan Kwashe Tsawon Lokaci Suna Zaman Dadaro, Matashi Ya Wartaki Budurwar sa, Ya Bayar Da Dalilai
Ya bayyana cewa ya shiga shekarar 2023 da ƙafar dama saboda ya samu soyayyar baturiyar.
Bidiyon wanda baya da tsawo sosai ya nuna yadda masoyan biyu suke nunawa junan su ƙauna, cike da kulawa da annashuwa.
Matashin ya bayyana cewa suna matuƙar ƙaunar junan su, kuma suna jindaɗin kasancewar masoya.
Bidiyon ya burge mutane sosai inda wasu suka yaba musu yayin da wasu kuma suka yi akasin hakan.
Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin da mutane suka bayyana waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
@Nikki Benz ya rubuta:
“Instagram da nima nake tayi, wai ya akayi ne lamari na ya bambanta da na saura.”
@millerlee03 ya rubuta:
“Ƴallaɓai ta taimaka ta haɗa ni da ƙawarta.
@God’s Ambassador ya rubuta:
“Daga ina take ne?”
Dabarar Da Na Yiwa Malamin Da Yake Son Yayi Lalata Da Ni -Wata Ɗaliba
A wani labarin na daban kuma, wata ɗaliba ta bayyana wata dabara da ta yiwa malamin da yake so yayi lalata da ita.
Wata budurwa wacce lakcaranta yake ƙoƙarin yin baɗala da ita tayi wata dabara domin kauce masa.
A wani bidiyo da ta sanya budurwar ta bayyana cewa sai da tayi ƙaryar cewa tana da aure domin kaucewa abinda lakcaran yake so yayi da ita.