By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Lahadin data gabata ne wasu sojoji suka mamaye al’ummar Tungan-Maje dake unguwar Gwagwalada a Abuja, inda suka lakada wa Salihu Aliyu, Galadima da ‘yan uwansa duka.
Jaridar Aminiya ta gano cewa mutane takwas da suka hada da wata dalibar Kwalejin Ilimi (COE) Zuba mai shekaru 23, Shemau Salihu, tare da babban dan Galadima na Tungan-Maje, Abdulrahman Salihu, sun samu raunuka sakamakon dukan da aka yi musu.
Da yake bayyana wa wakilinmu yadda lamarin ya faru a ranar Litinin, Salihu yace yana zaune a kofar gidansa tare da mahaifinsa da wasu abokansa, kwatsam sojoji suka sauko daga motar Hilux suka dake shi da sanda.Yace sojojin sun raba kan su gida-gida, inda ya kara da cewa yayin da wasu ke cin zatafin su, wasu kuma sun shiga gidaje uku suna lakada wa mutanen da ke cikin su duka.
Yace a lokacin da yake tambayar matar ko menene matsalar da kuma wanda suke nema, sai aka shiga zazzafar muhawara.A cewarsa, bayan mutanen sun tafi ne sojojin suka afkawa al’ummar yankin.sannan Ya kara da cewa, ya gama sallar isha’i ne a lokacin da sojojin suka far wa yankin.
Kazalika Ya ce daga baya sojojin suka ja shi su ka sashi a cikin motar Hilux tare da wasu mutane bakwai zuwa bariki dake yankin.sai dai kuma bayan an sallame su, ya zarce zuwa wani asibiti dake unguwar domin yi masa magani.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Basaraken Tungan-Maje, Alhaji Salihu Isiaku Na ’Annabi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace yana fadarsa ne sai wasu daga cikin mutanensa suka zo wurinsa suka ce sojoji sun yi wa Galadima dukan tsiya da kuma wasu mutanen.
Shima anasa bangaren Mataimakin shugaban karamar hukumar Gwagwalada, Alhaji Mohammed Kasim Ikwa, ya tabbatar wa da wakilinmu faruwar lamarin, inda yace ya ziyarci al’ummar garin nan take ya samu labarin faruwar lamarin.“A gaskiya ina Tungan-Maje da safiyar yau, sai suka kira ni yayin da wasu sojoji suka mamaye gidaje uku tare da lakada wa wasu mazauna garin duka.
Sannan mataimakin shugaban, yayin da yake Allah wadai da lamarin, yace yana kira ga kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, CP Sunday Babaji, domin ya sanar da shi lamarin.