Wani mutum ya zama abin magana a manhajar Instagram bayan ya haɗa mota da sanduna sannan ya sanya mata inji.
A cikin bidiyon wanda wani shafi mai suna BCR Worldwide ya sanya a Instagram, matashin ya shiga cikin motar sannan ya tayar da ita. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA: Garin neman gira: ango ya sha ƙasa yayin ƙoƙarin ɗaukar amaryar sa
duk da cewa ba a san tsawon lokacin da ya kwashe yana ƙoƙarin haɗa sandunan domin samar da motar ba, wasu mutane da yawa sun yaba masa bisa wannan namijin ƙoƙarin da yayi.
Sai dai wasu kuma sun ce sam basu ga wani abun a zo a gani ba a abinda matashin yaro saboda ba wata fikira da ya nuna.
Duk da hakan dai, matashin ya tuƙa motar sa a gaban mutane waɗanda cikin ɗoki suka taru domin ba idon su na abinci.
Bidiyon ya nuna yadda ya tayar da motar kamar babur kafin ya fara tafiya da ita.
https://www.instagram.com/reel/Cm_rg9LJ5X9/?igshid=YmMyMTA2M2Y=
Bidiyon na motar sanduna mai taya huɗu mutane sun yi sharhi sosai a kan sa.
Ga kaɗan daga ciki:
@donrabtob ya rubuta:
“Mutumina, wannan abin a yaba ne. Ka huta da cinkoson Legas.
@poolerena ya rubuta:
“Lallai, da haka fa motoci suke farawa. Sannan kuma ku sani mota fa doki ce da siddi.
@corneliusogunsalu ya rubuta:
“Har yanzu akwai mutane masu yabawa sakarci. Wannan kamata yayi ace wani abinda yaran makarantar raino za su haɗa ne da kayan aikin da suka dace.
Aure Akwai Daɗi, Na Sha Baƙar Wuya Lokacin Da Nake Gwauruwa -Wata Matashiya
A wani labarin na daban kuma, wata matashiya ta bayyana gagarumin sauyin da ta samu daga rayuwar gwauranci zuwa ta aure.
Wata matashiya ta sanya wani bidiyo a Instagram inda ta taya kanta murna bayan ta samu tayi aure.
A cikin bidiyon wanda matashiyar ta sanya a shafinta na Instagram mai suna @unique.aiphy, matashiyar mai suna Ifunanya Ochei ta bayyana cewa ta sha baƙar wuya lokacin da take gwauruwa