Yadda Wata Budurwa Ta Yi Ma Wani Saurayi Wayau Ta Karbi Miliyan 1.5 Daga Haduwa A Yanar Gizo
Rundunar ‘yan sandan jihar Osun a ranar Larabar nan ta kama wata yarinya ‘yar shekara 17 da ta cuci wani abokin ta da suka hadu a shafukan sada zumunta, inda ta gayyace shi zuwa Osun tare da yi masa fashin Naira miliyan 1.5.
Kwamishinan ‘yan sandan, Kehinde Longe a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sandan da ke Osogbo, ya ce mutumin Wanda aka cuta a garin Ikire, karamar hukumar Irewole ta jihar daga Legas ya shigar da kara bayan an yi masa fashi.
KARANTA WANNAN LABARIN:Dalilin da ya sa Atiku ya ke fushi da ni, da mambobin G-5 – Ortom
A cewarsa, wanda ke karar ya hadu da wadda ake zargin a shafukan sada zumunta kuma yana ta hira da’ita, inda ta gayyace shi zuwa inda take, tare da yi masa fashi.
An karbi wayar wanda ta cuta kuma sun fitar da kudi daga asusunsa a yayin bincike, an kama wasu mutane biyu, Ariyo Abayomi, 32 da Adeleke Opeyemi, mai shekaru 24, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu nan ba da jimawa ba.
Hakazalika, an gurfanar da wasu mutane takwas da ake zargi kan fashi da makami.
Obinna Chihuzo, 33, Igwe Chukwudi, 41, Ogbonna Destiny, 28, Eze Nwaze, 40, Olamilekan Samson, 30 da Kola Akinolu, 29, an kama su da laifin fashi da makami da suka addabi masu ababen hawa a kan titin Osun/Ife express, ciki har da Pistol (Turanci). An kwato bindigar ganga biyu na cikin gida, wayoyi iri-iri, kwamfutoci da sauran abubuwa daga cikinsu.
Abdulwasiu Jato, mai shekaru 47 da Kolawole Iwalaye, 39, an gabatar da su ne bisa laifin karbar motocin sata, da suka hada da mota kirar Toyota Camry (Muzzle) 2009 mai rijista da KUJ 619 DB da Toyota Corolla, 2012 mai rijista da KSF 407 HW.
A wani labarin kuma:Dalilin da ya sa Atiku ya ke fushi da ni, da mambobin G-5 – Ortom
Tsohon gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom, ya ce tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya fusata da shi saboda kasancewar sa na kungiyar G-5, da kafa dokar kiwo a jihar Benue da dai sauransu.
Tsohon Gwamnan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Makurdi ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Terver Akase, yana mayar da martani ne ga wata sanarwa da aka baiwa mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Mista Phrank Shaibu, wanda ake zargin ya caccaki mambobin G – 5 domin nuna adawa da nasarar da dan takarar shugaban kasa na PDP ya samu a zaben.