Wata ƙaramar yarinya ta ɗauki hankula sosai bisa yadda ta iya sarrafa kayan kwalliya kamar wata babbar budurwa.
Bidiyon ƙaramar yarinyar ya ɗauki hankalin masu amfani da manhajar TikTok, saboda yadda take ɗaukar kwalliya da kanta.
Yarinyar ta tafi da zuciyar mutane da daa sannan ta nishaɗantar bisa yadda take nuna tsarin yin kwalliyar ta ta. Renenshimba shine wanda ya sanya bidiyon na ta. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA: Ɗan albarka: Matashi ya gwangwaje mahaifiyar sa da katafaren gida
A cikin bidiyon mai tsawon daƙiƙa 51 wanda aka sanya a ranar 1 ga watan Janairu 2023, an ga yarinyar tsaye gaban madubi da riƙe da man leɓe.
Ta bayyana a cikin bidiyon cewa tana so ta kula da fuskarta sosai ta yadda zata ɗauki wanka iya wanka zuwa coci.
A cewar ta, tana kuma son tayi kyau iya kyau kamar wata gimbiya, hakan shine ya sanya take yin kwalliyar.
Ƙarfin hali da ƙwarin guiwar da yarinyar da ta nuna da kuma yadda take abubuwa kamar wata babbar budurwa shine abinda ya ɗauki hankulan mutane sosai.
Tuni bidiyon har ya karaɗe yanar gizo inda a manhajar ta TikTok mutum dubu shida da ɗari bakwai suka danna masa alamar so.
Mutane da dama sun yabawa yarinyar
@lindafruitfulballah ta rubuta:
“Shin wannan yarinyar ƙarama ce ko babba? Ina matuƙar son ta.”
@itsonly_jessicah ta rubuta:
“Na ji daɗin yadda tace kanta take yi mawa.”
@lucy said ta rubuta:
“Wannan tafi kowa kyau a cocin.”
Rashin Miji Na Damuna, Na ƙosa Nayi Aure -Kyakkyawar Budurwa Ta Koka
Wata kyakkyawar budurwa ƴar Najeriya ta koka a kafafen sada zumunta kan yadda har yanzu bata samu mijin aure ba.
Kyakkyawar budurwar wacce ke amfani da sunan Chris Amrah a manhajar TikTok, ta sanya wani bidiyo inda take cewa ta gaji matuƙa da zama babu miji sannan ta ƙosa tayi aure domin ta ji abinda ake ji a rayuwar aure.
A cewar ta, ta ji abubuwa da dama akan aure, masu kyau da marasa kyau, amma duk da hakan tana son ta ji ya ake ji idan anyi aure da kuma zama a ƙarkashin ikon mijinta.