Wata Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Najeriya ta karbe satifiket na Wani dalibi kan kama shi da hannu a Kungiyar asiri
Hukumomin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kwara, Ilorin, sun amince da janye takardar shaidar kammala Diploma ta kasa na AbdulRasheed Zubair Olatunji na sashen kula da harkokin mulki na makarantar nan take bisa zarginsa da hannu a kungiyar asiri.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tinubu Ya Gargadi Hukumomin Tsaro Akan Rike Bayanan Sirri
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakin magatakarda na ofishin magatakardar makarantar Olayemi Olatomi, ya fitar kuma ya sanya wa hannu a ranar Litinin da ta gabata kuma aka mika wa manema labarai a Ilorin.
Sanarwar ta bayyana cewa an yanke hukuncin ne bisa rahoton kwamitin ladabtar da daliban makarantar.
Hukumar ta ce shigar AbdulRasheed a harkar Kungiyar asiri ya nuna cewa bai da dabi’a kuma Bai cancanta ya samu takardar shedar makarantar.
Sanarwar ta kuma kara da cewa an dakatar da AbdulRasheed daga yin Shirin NYSC.
A wani labarin kuma:Majalisar Dattawa Ta Amince Da Bukatar Tinubu Na Nada Hadimai Guda 20
Majalisar dattawa ta amince da bukatar shugaban kasa Bola Tinubu na nada mashawarta na musamman guda 20.
Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya karanta bukatar shugaban a zauren majalisar a ranar Talata kuma an amince da ita ta hanyar kada kuri’a yayin zaman majalisar.