Hukumar da ke yiki da masu yi wa tattalin arzikin Kasa zagon Kasa EFCC a ranar Talatar nan ta gurfanar da wasu ma’aikatan banki guda biyu Freeman Jacob da Umar Abdullahi a gaban mai shari’a Akgah Amobeda na babbar kotun tarayya da ke Kano.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa An gurfanar da matasan biyu bisa tuhumarsu da laifuka uku da suka hada da hada baki da satar kudi.
DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Hukumar ta kuma gurfanar da wasu mutane biyu Ahmad Bashir da Abdulhakim Musa wanda aka fi sani da Gandu a gaban kuliya bisa laifin yin aiki tare da mitanen biyu a shekarar 2020.
KARANTA WANNAN Wata Kotu Ta Tura Wasu Matasa Gidan Maza
A cewar hukumar wadanda ake zargin sun hada baki ne a tsakaninsu wajen samar da katin cirar kudi na ATM da sunan wani Alhji Sani Muntari.
Haka kuma suka yi amfani da katin wajen sace makudan kudi Naira miliyan 20,000 a bankinsa.
Daya gada cikin tuhume-tuhumen da ake musu ta ce “Kai Freeman Austin Jacob, da Umat Abdullahi a wani lokaci a watan Fabrairun 2020 a Kano da ke yanki karkashin wannan kotu mai girma, kun hada kai da Ahmad Bashir da Abdulhakim Musa kan wajen samar da katin ATM”
Kun yi wannan abu daga asusun ajiyar bankin kasuwanci mallakin wani Alhaji Sani Muntari ba tare sa sani ko izinin wannan abokin ciniki ba, kuma laifin da za a yi hukuncinsa a karkashin sashi na 14 (7) na dokar intanet.
Wadanda ake tuhumar sun aikata wannan zamba ne ta hanayar amfani da ka layin waya mai asusun ajiya, wanda Bashir da ake tuhuma na uku ya sace, aka samar da katin ATM tare da taimakon wadanda ake kara na daya da na biyu.
Bincike ya gani wasu kudade da aka samu na satar a asusun bankin wanda ake kara na hufu, Abdulkarim Musa abokin wanda ake kara na uku Ahmad Bashir.
Sai dai wadanda ake kara sun musanta aikata laifin.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Bayan sauraren bayanan da bangarorin suka gabatar mai shari’a Amobeda ya bayar da umarnin a cigaba da tare wadanda ake kara sannan ya dage sauraren karar zuwa ranar 26 ga watan Yuni, 2023 domin ci gaba da sauraren bukatar beli da khma fara shari’ar.
A Wani Labarin Kuma Gwamnan Sokoto ya gana da shugabannin tsaro kan harin ‘yan bindiga
Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, a ranar Litinin, ya kira wani taron gaggawa na tsaro kan hare-haren da aka kai ranar Asabar da suka yi sanadin mutuwar mutane 37 a yankin arewacin jihar.
Jaridar The PUNCH ta ruwaito cewa a ranar Asabar din da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wasu kauyuka uku a karamar hukumar Tangaza da kuma wasu biyu a karamar hukumar Gwadabawa.