Yajin Aiki: Malaman Kwalejojin Ilmi sun baiwa Gwamnatin Tarayya kwanaki 21
Malaman Kwalejin Ilmi dake faɗin Ƙasa a ƙarƙashin Ƙungiyar Malaman Kwalejojin Ilmi sun baiwa Gwamnatin Tarayya kwanaki 21 data biya masu buƙatun su, ko kuma shirya shiga yajin aikin baba ta gani.
Ƙungiyar ta bada wannan gargaɗi a cikin wata sanarwa da Mataimakin Shugaban Ƙungiyar dana Shiyyar Kudu Maso Yamma Olusegun Lana Suka fitar a ranar Laraba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ɗan Majalisa Mai Wakiltar Mazaɓar Kwankwaso, da wasu mutum 3 sun ƙyale NNPP, sun koma APC
Malaman sunce Gwamnatin Tarayya bata yiwa Malaman Ilmi adalci, kuma ta watsar da dukkanin al’amuran da suka shafi Ƙungiyar da Malamai.
Ƙungiyar ta karanto wasu buƙatu da Gwamnati a matsayin kasawar Gwamnatin Tarayya na sanya kwamiti na yarjejeniyar su ta Shekarar 2010, ƙin sanar da biliyan 15 data yiwa Malaman, da kuma sanya IPPIS akan UTAS a matsayin tsarin da suka fi amincewa dasu.
Ƙungiyar tayi kira ga masu ruwa da tsaki dasu yi kira ga Gwamnati tayi abinda ya dace kafin ƙarewar kwanakin, akan abinda suka ce babu kokwanto akan shiga Yajin Aiki.
Comments 1