Yajin Aikin ASUU: Gwamnatin Buhari ta kashe ilimi, mu zamu binne shi – NANS
Kungiyar daliban Najeriya NANS shiyyar Kudu-maso-Yamma, ta zargi shugaban kasa Mohammed Buhari da binne ilimi a kasar, inda ta ce a shirye take ta gudanar da jana’izar ta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Magidanci ya kashe wata Ƴar haya da wuƙa a Ondo
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kodinetan NANS kuma mai magana da yawun hukumar, Adegboye Olatunji da Awoyinfa Opeoluwa, bi da bi, a ranar Litinin.
Kungiyar daliban ta ce za su sake bin titina a cikin kwanaki masu zuwa.
Wani bangare na sanarwar ya kara da cewa: “Ya dace mu ja hankalin jama’a da sauran kasashen duniya game da cin mutuncin daliban Najeriya da gwamnatin Buhari ta yi.
“Muna son daliban Najeriya su kasance a shirye don daukar gagarumin mataki kan yajin aikin ASUU. Mu a fili muke cewa wannan gwamnati ta sabawa ilimi kuma hakan ya saba wa muradin miliyoyin dalibai da matasa.
“A kwanaki masu zuwa, za mu mamaye titunan yankin Kudu-maso-Yamma don gudanar da bikin jana’izar ilimin na karshe a kasar nan saboda abin da gwamnatin Buhari ke wakilta kenan,” in ji sanarwar.
A wani labarin kuma: 2023: Dalilin da yasa ambaton Tinubu ya cika Kafafen Yaɗa Labaru da Najeriya – Jigon APC, Oyalowo
Wani fitaccen dan jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Ayo Oyalowo, ya caccaki wadanda ke zargin Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, ba shi da koshin lafiya, inda ya bayyana cewa shi (Tinubu) ne ya kasance babban abin kallo a zaben shugaban kasa mai zuwa.
Oyalowo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi a shirin Siyasar Yau na Channels TV.