Biyo bayan takun saka tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU na tsawon watanni bakwai, kungiyar dalibai ta kasa NANS ta bayyana aniyar ta na dakatar da aiki a dukkan filayen jiragen sama na kasa da kasa.
Kungiyar NANS ta kasa ta yi taro a karshen mako a Akure, babban birnin jihar Ondo, inda ta yi Allah-wadai da yadda gwamnatin tarayya ke mu’amala da malaman da suke yajin aiki da kuma ilimi gaba daya.
Daliban sun yi ikirarin cewa an yi nasarar rufe manyan tituna na tsawon kwanaki hudu, dalilin da ya sa suka yanke shawarar dakatar da tafiye-tafiye zuwa kasashen waje daga ranar 19 ga Satumba, 2022, domin jawo hankalin gwamnati.
KARANTA ANAN: Najeriya Tana Mataki Na Karshe Na Rugujewa — Dan Takarar Shugaban Kasa
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa daliban zasu yi wannan aiki ne domin mahukunta su fuskanci wahalar da daliban suka sha na watanni bakwai da suka gabata.
Shugaban Hukumar NANS na “Karshen Yajin aikin ASUU Yanzu”, Ojo Raymond Olumide, ya bayyana cewa tuni daliban sun gaji da rokon bangarorin biyu kan wajibcin kawo karshen yajin aikin a yayin wata ganawa da manema labarai.
“Dole ne gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta warware duk wasu basussukan da ake bin malamai da kuma albashin malamai”, Olumide, ya kara da cewa filayen jiragen saman da za a mamaye za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai an janye yajin aikin.
A wani labarin kuma: Mataimakin Shugaban Kasa Zai Wakilci Najeriya A Wajen Jana’izar Elizabeth
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, SAN, zai wakilci Najeriya a wasu taruka a gobe da kuma ranar litinin, a yayin jana’izar marigayiya Sarauniya Elizabeth ll a kasar Ingila.
Osinbajo zai bar Abuja ne a ranar Asabar din nan don halartar taron dangin sarauta, da shugabannin kasashen duniya – ciki har da mambobin kungiyar kasashe rainon Ingila, shugabannin kasashe duniya, manyan gwamnoni, firaministoci, da kuma iyalan sarakunan kasashen waje – a wajen bukukuwan, ciki har da bikin jana’izar da aka shirya gudanarwa a Westminster Abbey ranar Litinin.