Wasu ƴan Najeriya sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari data biya Malaman Jami’o’i haƙƙoƙin su domin magance yajin aiki da ake gudanarwa a halin yanzu.
Wasu Ɗalibai a Abuja sun nuna ɓacin ransu akan yawaitar yajin aiki, inda suka ce yawan yajin aikin baya da kyau da kuma kawo tsaiko a cigaban ilmi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kuyi maza ku janye Sojojin ku daga Ukraniya — Najeriya ga Rasha
Wani Malami a Kwalejin Ilmi ta citi dake Abuja Mr Samuel Onime yayi gargaɗin cewa Yajin Aiki yana da yiwuwar sanya ɗalibai su shiga ta’addanci, da kuma kawo taɓarɓarewar tsaro a Ƙasar.
Ya shawarci Gwamnatin Tarayya data cigaba da tattaunawa sa ASUU da manufar biya masu haƙƙoƙin su.
Onime yayi kira ga Ɗalibai dasu nemi sana’a, domin su zamanto suna wani aikin kafin a kira yajin aiki.
Mr Mark Asekhemhe wani ɗalibi yace yajin aikin ya kawo koma baya a harkokin karatu a Jami’o’i.
Comments 1