Gwamnatin Tarayya tayi taro da tawagar ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki guda 7 wato G7 dake Najeriya, inda ta bayyana rashin jindaɗi akan faɗan Rasha da Ukraniya tare da yin kira ga zaman lafiya domin magance faɗan dake faruwa.
Ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama yayi taron da tawagar a ranar Juma’a a Abuja, yana mai kiran zaman lafiya, tare da amfani da tsarin Diflomasiyya wajen magance bambance-bambance.
Onyeama yace Najeriya bata amince da amfani da Makami ba wanda Rasha ke yi, inda yayi kira ga Rasha data janye sojojin ta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar Kare Hakkin Mai Siye A Kano, Ta Kama Wani Sojan Gona Mai Damfarar Jama’a
“Zaman lafiya da tsarin Diflomasiyya shiya kamata ƙasashen sufi ɗabbaƙawa.
“Muna goyon bayan duk wani yunƙuri na hana amfani da karfin soji, sannan Sojojin Rasha su dawo Ƙasar su,” inji Onyeama.
Dayake jawabi ga Manema Labaru bayan taron sirri, Wakilin Ƙasar Germany a Najeriya Birgitt Ory, Wanda Kuma shine Shugaban su, ya yaba da ƙungiyar Afirka akan jawaban ta akan lamarin.
Ory, wanda ya Yabawa Najeriya data sanya ƙarfin ta, yace Najeriya ƙasa ce mai mahimmanci da Duniya ya kamata ta saurara