Daliban jami’ar Fasaha ta Gwamnatin tarayya dake Akure, a jihar Ondo, a yau Litinin sunyi Wani gangamin tare hanya da nufin nuna bacin ransu.
Daliban dai sunyi tururuwa ne inda suka tare babbar hanyar Akure zuwa Ilesa, suna zanga-zangar adawa da yajin aikin Kungiyar ASUU.
Baya ga haka, wasu daga cikin daliban sun toshe kofar shiga Jami’ar a yau Litinin da nufin hana kowa shiga ciki.
Wannan mataki da daliban suka dauka ya tilasta haifar da cinkoson Ababan hawa masu mu’amala da wurin da abun ya faru.
Daliban dai dauke suke da kwalaye masu rubuce rubuce kala kala, wanda suke nuna irin yadda suka gaji da zaman gida.
Da yake ganawa da manema labarai shugaban kungiyar daliban jami’ar Mr Abiodun Ibiyemi ya ce baza su ci gaba da zuba idanu ASUU na neman kai su ƙasa baki daya ba.
Ya ce Domin ceto tarin daliban dake zaune a gida ba tare da sanin abun yi, ya kamata mahukunta su gaggauta daukar matakan kawo karshen wannan yajin aiki na ASUU.