By Ishaq Dabai
Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) ya bukaci Direbobin Tankar Man Fetur dasu janye yajin aikin da suke shirin yi, tare da yin alkawarin zuba jari wajen gyaran manyan hanyoyi a fadin kasar nan.
Wannan alkawarin ya zo ne sa’o’i 24 kacal kafin fara yajin aikin da Kungiyar Ma’aikatan Man Fetur ta Kasa (NUPENG) ta kira don nuna rashin amincewar su da mummunan titin jihohi a fadin kasar.
NUPENG ta yi ikirarin cewa ya dauki kusan kwanaki biyar zuwa shida kafin tankar man fetur ta tashi daga Legas zuwa Abuja saboda “abin kunya na rashin kyawun hanyoyi”.
Kungiyar zata fara yajin aikin ne ranar Litinin. Najeriya na safarar mafi yawan kayan man fetur miliyan 65 a kowace rana ana amfani da babbar Motar waje daukar (fetur) ta hanya saboda rashin kyawun bututun mai wanda yake sanadiyar barna mai yawa.
Kamfanin NNPC a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi ta Babban Manajan Rukunin, Mista Garba Deen Muhammad ya bukaci direbobin dasu dakatar da ci gaba da shirin tafiya yajin aikin don maslaha da jin dadin al’ummar Najeriya.
Kamfanin ya bayyana cewa “duk da cewa ba alhakin NNPC bane na gina ko gyara hanyoyi, duk wani katsalandan a cikin gurbata albarkatun man fetur zuwa sassa daban -daban na Najeriya zai yi illa ga harkar NNPC da kuma kawo hadari ga samar da makamashi, wanda kasar ke yi.
Mista Muhammad ya yi bayanin cewa “babban abin da NNPC ta sa baki a kai shi ne samar da kudade masu yawa don sake gina hanyoyi ta hanyar abin daya dace da Harajin.
Kamfanin NNPC ya yi kira ga Direbobin “dasu gaggauta dakatar da sanarwar yajin aikin tare da baiwa kokarin gwamnati da hukumomin damar magance kalubalen don amfanin kowa.