By Ishaq Dabai
Da yammacin jiya Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, yake duba yadda aka fara aikin ginin manyan makarantun sakadire da za’ayi a masarautu biyar na Jihar Kano.
Gwamnan ya fara da duba yadda aka fara aikin na masarautar Kano a filin Bola dake court Road bisa kulawar kwamishinan ma’aikatar ilimi, Hon. Sanusi Sa’id Kiru.
Gwamnan ya bayyana kudirin sa na ganin an kammala ginin makarantun sakadiren domin ya shirya tsaf ta yadda za’a iya karbar daliban da za’a yaye daga makarantun firamare duba da yadda ilimi ya zama kyauta kuma dole a fadin Jihar Kano.
A jawabin sa, kwamishinan ilimi, Hon. Sanusi Sa’id Kiru ya bayyana yadda akayi tunani aka dauko tsarin ginin da babu irin sa ta yadda makarantar zata iya samawar kanta kudaden shiga domin cigaba da inganta harkokin ilimi.