Babban Darakta na Cibiyar Bunkasa Albarkatun Dan Adam da Karfafa kirkire kirkire a Kaduna, Dr Mohammed Ali, ya ce Arewa ba ta bukatar hukumar almajirai, sai dai a hana almajiranci baki daya. Kamar yadda Punch ta ruwaito
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin wakilai daga cibiyar raya almajiri da karfafa musu gwiwa ta Ayana Centre for Almajiri Development and Empowerment Initiative a wata ziyara da suka kai ofishin sa ranar Lahadi a Kaduna.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Hukuncin Shekara Daya, Da Tarar Nair 500,000 Na Dakon Masu Siyan Kuri’u — INEC
Tun da fari akwai Kudirin kafa hukumar da za ta magance almajirci da sauran yaran da ba sa zuwa makaranta, tare da daukar nauyin matakin karatu na biyu a majalisar wakilai, da aka gabatar a ranar 23 ga watan Nuwamba.
Yaran mabaratan da aka fi sani da almajirai, galibinsu daliban makarantun kur’ani ne da aka fi sani da ‘tsangaya’ wadanda iyayensu ke baiwa malaman addinin Islama don neman karatun kur’ani.
Su kuma malamai su kan kwashe su daga gidajensu zuwa lungu da sako na wani gari ba tare da an tanadar musu wajan kwana da ciyar da su koyi sana’a, ko tufafin ba, inda a karshe su ke koma wa yin barace-barace.
Babban Daraktan Cibiyar Bunkasa Albarkatun Dan Adam da Karfafa kirkire-kirkire a Kaduna, Dokta Mohammed Ali, ya bayyana cewa barace-barace a kan tituna a matsayin matsala ce ta zamantakewa da tattalin arziki da kuma muhalli da ake gani sosai a biranen dake fadin jihar Kaduna, inda ya ce, ya zama ruwan dare a jihohin arewacin kasar nan
Ya koka da cewa halin da ake ciki a yanzu yana da ban tsoro saboda ba manyan mutane ne kawai ke aikata irin wannan ba, har ma da yara kanana.
Ya kara da cewa, wasu malamai, yan jaridai da wasu jama’a na danganta barace-barace da addinin Musulunci.
Ya bayyana cewa babu wani abu na Musulunci a cikinsa, sai dai sakamakon kasala, dogaro da wani, da dai sauransu.
Ya kuma jaddada cewa, “Musulunci addini ne mai kyau dake koyar da zamantakewa kuma ya samar da ka’idoji da tsare-tsare da mutum zai iya samun abin rayuwarsa ba sai ta hanyar bara ba.
A wani labari kuma, Da Hannun Mambobin Jam’iyar PDP Aka Kai wa Ofishin Mu Hari A Rivers — SDP
Wasu bata gari da ake kyautata zaton ‘yanbangar siyasa ne sun kai hari ofishin jam’iyyar SDP da ke karamar hukumar Tai a jihar Rivers da sanyin safiyar ranar Litinin.
Dan takarar gwamna a jam’iyyar SDP, Magnus Abe ne ya tabbatar da hakan a wata ganawa da manema labarai a Fatakwal, inda ya zargi shugabancin jam’iyyar PDP na karamar hukumar Tai da kitsa harin da nufin aiwatar da umarnin dokar sashi na 21 da 22 na gwamnatin jihar.