‘
Gwamman Yan gudun hijiran Rohingya da mafi yawansu maza ne sun isa gabar trkun Indusiya a Kwalekwalen katako da injin shi ya sami matsala. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
Hukumomin kasar ne suka bayyana hakan, inda suka ce, Kabilar dake da karancin Jama’a sun baro asalin gidajensu ne dake Myanmar
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Hukuncin Shekara Daya, Da Tarar Nair 500,000 Na Dakon Masu Siyan Kuri’u — INEC
Rahotanni sun nuna cewa, Masu neman mafakan na fama da tsananin yunwa da rashin garkuwan jiki saboda sun kwashe tsawon wata guda a teku yayin da tuni aka kai mutum asibiti.
Sai dai hukumomin na Indusiya ba su bayyana ko Mutanen na cikin Yan kabilar Rohingya 150 da suka makale a teku ba, a makwannin da suka gabata.
Kazalika da yake yiwa Kamfanin dillancin Labaran faransa karin haske, wani Jami’i a rundunar yan sandan kasar Mai suna Winardy ya ce, Kwale-kwalen katakon duake da mutane 57 sun Iso Lardin Aceh ne a safiyar ranar Lahadi.
A wani labari kuma, Yakamata A Dakatar Da Almajirci A Arewacin Najeriya — Dr Mohammed Ali
Babban Darakta na Cibiyar Bunkasa Albarkatun Dan Adam da Karfafa kirkire kirkire a Kaduna, Dr Mohammed Ali, ya ce Arewa ba ta bukatar hukumar almajirai, sai dai a hana almajiranci baki daya.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi bakuncin wakilai daga cibiyar raya almajiri da karfafa musu gwiwa ta Ayana Centre for Almajiri Development and Empowerment Initiative a wata ziyara da suka kai ofishin sa ranar Lahadi a Kaduna.