Jakadan Najeriya na musamman a Yankin Tafkin Chadi Ambasada Babagana Kingibe ya ce ana iya tattauna makomar kasar sakamakon barakar da ake samu daga yankuna daban daban wadanda ke bukatar sake fasalin yadda ake tafiyar da ita.
Kingibe wanda ke jawabi wajen bikin karrama shi da akayi birnin Lagos, yace ko da tsakanin mata da miji akan tattauna yadda zamantakewar su ke tafiya, saboda haka babu dalilin da za’a ce ba za’a iya tattauna makomar hadin kan Najeriya ba.
Sai dai tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar ya shaidawa masu bukatar raba Najeriya cewar, babu yadda za’a iya tsaga kasar da masu fafutukar raba Najeriya ke bukata koda kuwa an karkasa ta.
Kingibe ya bayyana cewar a Najeriya aka haife shi, kuma a kasar ya girma, kana shi da mutanen da suka yi rayuwa da shi na ci gaba da amincewa da dorewar kasar.
Jakadan yace ya san akwai wasu daga cikin abokan tafiyar sa da suke ganin bai dace a tattauna makomar kasar ba, inda yake cewa hakan ba daidai bane, domin koda auren mace da namiji ne akan tattauna akai idan bukatar haka ta taso domin gyara yadda ake tafiya.
Kingibe yace duk lokacin da wani bangare ya bayyana cewar baya bukatar ci gaba da zaman da akeyi, sai a taimaka masa wajen fahimtar da shi muhimmancin zamantakewar da kuma illar rabuwar domin bashi damar nazari akai.
Jakadan ya bukaci masu neman ballewa daga Najeriyar da su sake nazari akan bukatar su da abinda ke iya biyo baya.