By Abbas Yakubu Yaura
Daruruwan mazauna yankunan kan iyaka da Taraba sun tsere daga gidajensu bayan kashe mutane 11 ciki har da wani basaraken gargajiya da sojojin Ambazoniya suka yi.
Sojojin sun kai hari kan wasu al’ummomin kan iyaka a karamar hukumar Takum ranar Laraba inda suka kashe mutane 11.
Sojojin na Ambazoniya sun kuma kona gidaje da makarantu da dama tare da kwashe dukiyoyi.
Shugaban karamar hukumar Takum Mista Shiban Tikari, yace an gano gawarwakin wadanda aka kashe biyar, sannan wasu da dama sun bace.
Sannan yace an tsara sojoji daga Takum don kare al’ummomin kan iyaka daga ‘yan aware da kuma sojojin Kamaru dake kai hare-hare kan al’ummomin kan iyaka a kananan hukumomin Kurmi da Takum na jihar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a watan daya gabata, sojojin Kamaru sun kori wasu kauyuka uku dake kan iyaka a karamar hukumar Kurmi ta jihar bisa zargin neman ‘yan awaren Ambazoniya.