Gwamnatin jihar Sakkwato a ranar Asabar ta bayyana cewa ya zuwa yanzu akalla ‘yan bindiga 210 ne suka tuba tun bayan kaddamar da shirin sulhu da ‘yan bindiga a jihar.
Kwamishinan jihar akan abin da ya shafi tsaro, Ritaya Kanal garba Moyi shi ne ya bayyanawa manema labarai hakan a Sakkwato.
Moyi, wanda shi ne yake jagorantar shirin sulhun, ya ce sun yi nasarar ganin an saki dukkanin wadanda ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.
A cewarsa, wadanda aka saki wadanda mafi yawansu ‘yan asalin jihar Sakkwato ne, sai dai akwai wadansu daga jihohin Kebbi da Zamfara da Jamhuriyyar kasar Nijer, inda ya ce tuni kuma aka hada su da iyalansu.