Wadansu fitattun ‘yan Nijeriya sun nuna goyon bayansu ga gwamnatin Muhammadu Buhari bisa rufe kan iyakokin kasar da ya yi domin ganin an bunkasa tattalin arziki Nijeriya.
Sun nuna goyon bayan na su ne a wani taro na shekarar 2019 wanda gamayyar Ma’aikatan Banki na Nijeriya wato suka shirya a garin Legas. Wato a taron ‘Investiture of the Chartered Institute of Bankers of Nigeria (CIBN)’ a turance.
Taken taron shi ne; “Nigeria’s Emerging New Economy: Opportunities, Challenges and Prospects.” Wato Sabuwar Dabarar Tsimi da Tanadi: Damammaki, Kalubale da kuma abin da ake fatan cimma’
Tsohon Babban Sakataren kungiyar kasashen renon Ingila, Cif Emeka Anyaoku, ya ce rufe kan iyakokin Nijeriyar, zai bunkasa tattalin arzikin Nijeiriya. Ya ce; “muna goyon bayan rufe iyakokin Nijeriya da shugaba Muhammadu Buhari ya yi musamman idan aka yi duba da amfanin haka ga ci gaban kasa.” In ji shi.
Ya kara da cewa; akwai bukatar gwamnati ta sa ido sosai domin ganin kasar ta samu ci gaba ta fuskancin noma da ma’aikatun noman. Tare da bunkasa bangaren samar da abincin da ka iya ciyar da ‘yan Nijeriya.