By Abbas Yakubu Yaura
A jiya ne gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da mutuwar matafiya 23 a wani hari da ‘yan bindiga suka kai a karamar hukumar Isa ta jihar.
Hakan ya zo ne a daidai lokacin da Majalisar Dattawa ta nuna alhinin rasuwar matafiyan da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kona kurmus a ranar Litinin a hanyarsu ta zuwa Gayan a Jihar Kaduna.
Har ila yau, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya jajanta wa takwaransa na Sokoto, Gwamna Aminu Tambuwal, da gwamnati da al’ummar jihar kan kisan gillar da aka yi wa matafiyan.
A halin da ake ciki, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana bakin cikinsa dangane da munanan hare-haren da ake kaiwa wasu matafiya a jihar Sokoto.
Martanin na shugaban kasar yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Mista Femi Adesina ya fitar ranar Laraba a Abuja.
“Na damu matuka game da yadda aka kai wa wadannan ‘yan kasa hari, a yayin da suka yi tafiya ta halal zuwa wani yanki na kasar nan.
“Wannan ya nuna cewa mugunyar da wannan gwamnatin ke fuskanta shine wanda ke bukatar goyon baya da kuma shigar da dukkan ‘yan Najeriya,” inji shi.
Shugaban ya jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, yana mai tabbatar da cewa jami’an tsaro za su ci gaba da bayar da gudunmowarsu wajen ganin an kawo karshen ayyukan ‘yan ta’adda.
Mai baiwa Gwamna Tambuwal shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Malam Muhammad Bello, yace gwamnatin jihar ta bullo da matakai da sabbin dabaru don dakile afkuwar lamarin nan gaba ta hanyar hada kai da hukumomin tsaro.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Sabanin rade-radin da ake yi cewa sama da mutane 40 ne suka rasa rayukansu a wani harin da ‘yan bindiga suka kai kan wata motar bas mai dauke da mutane 42 da ke kan hanyar zuwa Kaduna a ranar Litinin, bayanai sun nuna cewa mutane 23 ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai kauyen Gidan Bawa dake karamar hukumar Isa ta jihar Sakkwato. A cewar Bello.
“Gwamna Ortom ya jajantawa Gwamna Tambuwal da al’ummar jihar Sokoto tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda abin ya shafa, ya kuma baiwa iyalai hakurin jure rashin da ba za a iya kwatantawa ba.”