Wasu ‘yan bindiga da ake zargin’ yan kungiyar asiri ne sun kai hari kan tawagar ‘yan sanda da ke sintiri a kan hanyar Kolo zuwa Ogbia a karamar hukumar Ogbia ta jihar Bayelsa.
An rahoto cewa wani sifeton ‘yan sanda ya samu rauni a harin yayin da aka kwace harsashe sa.
A cewar wata majiya daga yankin Kolo, lamarin ya faru ne mintuna kadan zuwa tsakar dare ranar Litinin.
Ya ce lokacin da mazauna garin suka ji harbin, sai suka yi tunanin ‘yan bindiga ne ke kai hari kan al’umma yankin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abin da yake bani tsoro a Harkar Fim, inji Zaharaddeen Sani
Kodayake akwai rahotannin da ba a tabbatar da su ba cewa, an kashe Sufeto na ‘yan sanda, amma kakakin rundunar yan sanda a jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya ce Sufeto ya samu rauni ne kawai.
Butswat, yayin tabbatar da faruwar lamarin a kafar sadarwa ta WhatsApp ga majiyar Jaridar Dimokuradiyya ya ce, ana ci gaba da bincike don ganin an kama wadanda suka Kai harin.
A wani labarin Kuma makamancin wannan
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe wani limamin cocin Baptist da kuma wani mutum daya a yammacin Litinin a Lisuru Gida, masarautar Ikulu dake karamar hukumar Zango Kataf ta jihar Kaduna.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar wa jaridar PUNCH faruwar lamarin a jiya, inda yace ‘yan bindigar sun bude wuta kan mutanen biyu a kan hanyarsu ta komawa gida daga gonakinsu da misalin karfe 6 na yamma.
Majiyar ta bayyana wadanda ake zargi da cewa Fulani makiyaya ne, inda ta kara da cewa al’ummar na fuskantar barazana.“Fulani sun mayar da gonakin mu wuraren kiwo kuma muna zama cikin barazanar tsaro.
Majiyar tace “al’ummomin dake makwabta koyaushe suna shakkar Fulanin yankin da muke gani a matsayin makwabtanmu ne su.”
Kazalika Ya ce al’ada ta dawo cikin al’umma yayin da yake kira ga gwamnati data ninka kokarinta na ganin an kamo wadanda suka aikata wannan danyen aikin.
A halin da ake ciki, na kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Jalige don yin tsokaci kan lamarin yaci tura har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Comments 1