Yan bindiga sun hallaka babban Soja a Jigawa
Wasu yan fashi da makami sun hallaka wani manjo a Jigawa
ASP Lawan Salisu Adam, Mai magana da yawun Yan sanda ya bayyana haka a wani sanarwa da ya fitar.
Yace lamarin ya auku ne a wani Kauyen Dunbudus dake Karamar hukumar Dutse a Jahar Jigawa da misalin karfe tara ranar Lahadi.
KARANTA:- Dubu 50 aka bani inkai buhu 173 na Wiwi Daura
Kamar yadda Lawan yace, jami’an suna kan hanyar zuwa Kaduna daga Borno.
A ranar 4 ga watan July ne aka sami sanarwar Yan fashin sun rufe hanyar Maiduguri zuwa Kano.
Yan sanda sunyi yunkurin kai dauki lokacin da suka sami labarin, sai dai koda suka isa Yan fashin sun bazama cikin daji.
Daya daga cikin masu rakiyar Manjon mai suna PTE Haris Aliyu an harbeshi a wuya, inda Manjo M. S Ismail suka kasheshi nan take.