An kashe wani malami mai suna Ahmed Saheed da dalibin digiri na farko a Kwalejin horas da Ilimin kiwon Lafiya ta Michael Otedola (MOCPED) da ke karamar hukumar Epe a jihar Legas.
An ce an kashe malamin ne a kusa da garin Poka da ke Epe, yayin da dalibin mai suna Razak Bakare kuma aka harbe shi a harabar kwalejin.
Wata majiyar ‘yan sanda ta shaida wa wakilin Jaridar Dimokuradiyya cewa, lamurorin, wadanda ya bayyana a matsayin abin takaici, sun faru ne cikin sa’o’i 48.
Yan majalisa da sarakunan gargajiya na yankin ne suka tabbatar da rasuwar malamin da dalibar kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Sun ce yayin da aka bindige dalibin aka kashe shi a ranar Laraba, an harbe malamin ne a ranar Juma’ar data gabata
A halin yanzu, akwai rashin jin daɗi a cikin al’ummar malaman Poka, a cewar Aladeshoyin na garin Odo-Noforija, a sashin Epe.
Oba Babatunde Ogunlaja, sarkin gargajiya na al’ummar, ya bayyana alhininsa kan faruwar lamarin.
Ya ce zaman lafiya a garin Noforija ya ruguje sakamakon kashe-kashen da aka samu.
Don haka ya Kuma yi kira ga mahukuntan cibiyar da su sanya na’urorin daukar hoton sirri, na Closed Circuit Television (CCTV) a cikin harabar makarantar da kewaye.
Ogunlaja ya kuma yi kira ga Gwamna Babajide Sanwo-Olu da kwamishinan ‘yan sanda, Hakeem Odumosu da su kara tura jami’an tsaro a cikin al’ummar yankin da Abun ya shafa.
Ya roki gwamnatin jihar Legas da ta sake gina katangar cibiyar da ta ruguje.
Shi ma Sarkin Alara na masarautar Ilara, Oba Olufolarin Ogunsanwo, ya yi Allah wadai da faruwar lamarin, ya kuma bukaci jami’an tsaro da su kamo wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Sai dai ya yi alkawarin cewa Masarautar gargajiya za ta tabbatar da cewa an dukufa wajen yakar irin wannan munanan da suke kaiwa al’uma hari.