Yan bindiga da ake tunanin yan ta’adda ne, sun kai hari a majami’ar Kogi, inda suka kashe wani mutum daya, tare da garkuwa da mutane uku.
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar da safe a cocin ECWA dake Okedayo, Kabba, hedikwatar Kabba a Karamar Hukumar Bunu ta jahar Kogi.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yan bindiga sun kashe yan sanda 3, sun raunata wasu a jahar Anambra
Idan dai ba’a manta ba, Gwamna Yahaya Bello ya ta’ba bayyana, jahar Kogi a matsayin jahar da tafi kowacce kwanciyar hankali a fadin Nigeria, kamar yadda majiyar jaridar Dimokuradiyya ta ruwaita
Haka zalika, kai harin ya faru ne, yan kwanaki kadan bayan kai hari a cibiyar gyaran akida ta Kabba, gami da sace masu kiwon kaji guda uku a gonar su.
Yan ta’addan sun kai hari a cocin a likacin da suke tsaka da gudanar da ibadojin su
Cocin dai na kan Babbar hanyar Kabba zuwa Okene.
A lokacin da aka tuntube shi, mai magana da yawun Rundunar yan sanda na jahar Kogi DSP William Aya ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace jami’an rundunar na akan hanyar gano wadanda suka aikata lamarin.