Wasu mutane ɗauke da bindigogi da ake kyau tata zaton yan bindiga ne sun kashe shugaban garin Nyaluna dake ƙaramar hukumar Wase ta jihar Filato.
Daily Post ta ruwiaito cewa, Maharan sun kuma farmaki wasu garuruwa biyu dake yankin.
KARABTA WANNAN LABARIN: An Kama Mutane 80 Da Ake zargi Da Taimakawa Yan bindiga – Gwamnatin Zamfara
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin Kakakin rundunar yan sandan jihar DSP Alabo Alfred, ya ce mutane uku ne aka kashe sandiyar harin, ya ƙara da cewa suna ci gaba ta tattara bayanai kan lamarin.
“Mutane uku ne aka kashe a lamarin a kauyen Nyalun da ke karamar hukumar Wase, amma ba mu da cikakken bayanin abin da ya faru a halin yanzu,” in ji shi.
Tun da fari Mazauna garin sun bayyana cewa yan bindigar sun kashe mutane ne a cikin kauyen lokacin da suka farwa garin a kan baburra, inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi.
Kazalika Mazauna garin sun faɗawa manema labarai cewa maharan da suka farmaki garin da misalin ƙarfe 8 na dare sun ɗauke mutane biyar daga garin waɗanda suka haɗa da mata biyu.
Shugaban matasan Wase Malam Shafi’i Sambo ya faɗawa jaridar Daily Trust cewa yan bindigar da suka zo da yawa sun kuma ɗauke baburra da dama.
A WANI LABARIN KUMA: Mayakan ISWAP Sun Fara Kafa Sansanoni A Zamfara— Gwamnatin Jihar Ta Koka
Rahotanni sun bayyana cewa an hangi ‘yan kungiyar ISWAP suna kafa sansanoni a kusa da kauyen Mutu da ke gundumar Mada na karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.
Shugaban kwamitin hukunta laifukan da suka shafi ‘yan fashi kuma mamba a kwamitin tsaro da tattara bayanan sirri na jiha, Dr Sani Abdullahi Shinkafi ne ya bayyana hakan a wani taro a Gusau.