Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da kama wasu mutane 80 bisa laifin taimakawa ‘yan bindiga. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
An dai tsare su ne bisa zarginsu da hannu wajen aikata fashi da makami da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
KAEANTA WANNAN LABARIN: Mayakan ISWAP Sun Fara Kafa Sansanoni A Zamfara— Gwamnatin Jihar Ta Koka
Abdullahi Shinkafi, Shugaban Kwamitin Hukunta ‘Yan Bindiga da Manyan Laifukan da ke da alaka da su, ya yi wa manema labarai jawabin hakan a ranar Talata.
Wadanda ake zargin da sojojin gwamnati suka kama, da suka hada da mata, sun kasance masu bayar da bayanai ne, da kuma masu samar da abinci, da kwayoyi, kayan soji da kuma kakin ‘yan sanda.
Shinkafi ya bayyana cewa jami’an tsaro na gudanar da bincike kan matakin da ake zargin su da aikatawa dake da alaka da miyagun laifuka.
“An riga an gurfanar da wasu a gaban kotu domin fuskantar tuhuma” kamar yadda NAN ta ruwaito.
Shinkafi ya kuma bayyana cewa, An samu nasarar kama ‘yan fashin da masu garkuwa da mutane ne sakamakon harin bama-bamai da rundunar sojin saman Najeriya ta kai a sansanonin su.
Shugaban ya ce an kashe da dama daga cikin barayin ko kuma an kore su daga maboyarsu.
Ya tabbatar da cewa rashin tsaro na daga cikin dalilan da suka sa gwamnati ta dakatar da gangamin siyasa da yakin neman zabe.
Shinkafi yayi Allah wadai da kashe-kashen da aka yi a kananan hukumomin Gusau, Tsafe, Gummi, Bukkuyum, Anka Bungudu, Maru, Maradun da kuma Kaura Namoda.
Ya kara da cewa, “Gwamnati ta kuma damu da kashe-kashen da aka yi wa wasu jami’an tsaron mu wadanda suka rasa rayukansu a wajen tsaronmu,” in ji shi.
A WANI LABARIN KUMA: Ku Dai Na Kaiwa Junan Ku Hare-Hare — INEC Ta Ja Kunnen Jam’iyun Siyasa
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta nuna damuwarta game da arangamar da ake samu tsakanin magoya bayan jam’iyun siyasan dake adawa da juna, yayin yakin neman zabe a fadin kasar nan.
Shugaban Hukumar Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a yau Talata yayin taron da hukumar ta shirya kan babban zaben shekarar 2023 mai zuwa.