Wasu ‘yan bindiga sun kashe Hakimin garin Sarkin Kudu a karamar hukumar Ibbi a jihar Taraba, Ali Hakimi.
An kashe Hakimi ne bayan wasu ‘yan bindiga 10 sun kai masa hari a fadarsa da ke garin Sarkin Kudu da misalin karfe 12:30 na safiyar Juma’a.
Karanta nanKungiyar Gwamnonin Arewa Ta Bayar Da Naira Miliyan 180 Ga Al’ummar Tudun Biri
Wani mazaunin garin, Bello Adamu ya shaida wa Aminiya cewa marigayin dan uwa ne ga Sarkin Kudun na Ibbi.
Adamu ya ce ‘yan bindigar sun kai hare-hare da dama a fadin masarautar tare da yin garkuwa da mutane da dama a baya-bayan nan.
Maharan sun tsere cikin daji bayan sun kashe hakimin kuma kowa da kowa a yankin na ficewa cikin tsoro saboda babu wanda ya san inda ‘yan bindigar za su kai hari a gaba,in ji Adamu.
Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan ba ta mayar da martani kan lamarin ba har ya zuwa lokacin da aka fitar da rahoton sakamakon rashin daukar waya da mai magan da yawun ‘yan sandan jahar bai yiba.
A wani labarin kumaJam’iyar PDP Na Neman Haddasa Rikici A Jahar Nasarawa-Gwamna Abdullahi Sule
Jam’iyyar PDP a jihar Nasarawa ta fuskanci suka daga Gwamna Abdullahi Sule, wanda ya zargi jam’iyyar adawa da tayar da tarzoma ta addini da kabilanci da gangan sakamakon hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na tabbatar da nasarar da gwamnan ya samu a zaben.
Babban mataimaki na musamman ga gwamnan kan harkokin jama’a, Mista Peter Ahemba, ya bayyana wadannan matsalolin yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a garin Lafia jiya.
Ahemba ya yi zargin cewa jam’iyyar PDP ta yi kamfen ne don bata sunan bangaren shari’a tare da kitsa zanga-zanga a babban birnin jihar biyo bayan hukuncin da kotu ta yanke na baya-bayan nan.