By Abbas Yakubu Yaura
Akalla an kashe mutane hudu tare da jikkata wasu da dama bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a unguwar Barawa dake karamar hukumar Batagarawa a jihar Katsina a ranar Lahadi.
Mazauna yankin sun ce maharan wadanda suka kai farmaki kauyen da misalin karfe tara na dare, sun kuma yi awon gaba da kayayyaki da dabbobin gida.
Al’ummar Barawa na da tazarar kilomita 10 daga birnin Katsina.
Sai dai kuma “Ba su yi garkuwa da kowa ba amma sun kashe mutum hudu, maza uku da wata tsohuwa.
“Wasu da dama kuma ‘yan bindigar sun jikkata su,” wani mazaunin garin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, yace.“Lokacin da ‘yan fashin suka tarwatsa rabin mutanen dake cikin al’umma, inda suka dinga bi gida-gida da kuma zuwa shaguna tare da dibar kayayyaki.
Majiyar tace “Sun yi awon gaba da duk kayayyakin dake cikin shagunan dake unguwar suka tafi da awaki da tumaki inda kuma suka bar mutanen da suka ji rauni awajen.”
“Mun yi jana’izar mutane hudu kuma mutane da dama sun samu munanan raunuka sakamakon harin,” in ji wani mazaunin garin.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa, bai amsa bukatar tabbatar da hakan ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Sai dai kwamishinan wasanni da ci gaban jama’a na jihar Katsina Sani Danlami ya tabbatar da faruwar harin, inda yace gwamnatin jihar ta samar da kayan agaji ga wadanda suka jikkata da kuma iyalan wadanda aka kashe.
Comments 1