By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga sun harbe Alhaji Sagir Hamidu, wanda tsohon dan takarar gwamna ne a jihar Zamfara a shekarar 2019.
An kashe shi ne lokacin da ‘yan bindiga suka tare hanyar Kaduna zuwa Abuja tare da bude wuta kan matafiya, a ranar Lahadi.
Jaridar Aminiya ta rawaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na rana kusa da Rijana a kan babbar hanyar data hada jama’a.
Shedun gani da ido sun tabbatar da cewa, tsohon Daraktan yarjejeniya na babban birnin tarayya Abuja, wanda kuma dan takarar gwamnan jihar Zamfara ne ya rasa ransa a saka makon faruwar lamarin.
Wasu shaidun gani da ido sun ce ‘yan bindigar sun shafe sama da sa’a guda suna cin karensu babu babbaka ba tare da kakkautawa ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja mai cike da ramuka da dama, ta zama tarkon mutuwa ga matafiya, wadanda ake kaiwa hari akai-akai; kodai a kashe su ko kuma a sacesu.
Sai dai ayyukan ‘yan bindigar ya ragu tun bayan da sojoji suka fara fatattakar ‘yan bindiga a wasu dazuzzukan jihar makonnin da suka gabata.
Wani faifan bidiyo da aka fitar ta yanar gizo a yammacin Lahadi ya nuna motoci biyu babu kowa wadanda da alamun an bar su a tsakiyar babbar hanyar ne.
Wani shaidan gani da ido dake tafiya a kan hanyar ya fitar da wani gajeren bidiyon dake nuna wasu motoci guda biyu da aka yi watsi dasu yayin da ake ta rade-radin cewa an sace mutanen cikinta.
Har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ba ta mayar da martani kan faifan bidiyon ba. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, bai amsa kiran da aka yi masa ba da kuma tattaunawa a kan bidiyon.