Yan bindiga sun sun kashe wani malami, mai Zakari Kigbu wanda kafin rasuwarsa yi aiki a kwalegin kimiyya da Fasaha ta Isa Mustapha Agwai dake garin Lafia, na Jihar Nasarawa.
Yan bindigar sun sace biyu daga cikin’ ya’ya mata a lokacin harin.
Kakkakin rundunar ‘yan sandan jihar Rahman Nansel ya tabbatar da aukuwar lamarin ga kafar da labarai ta Channel Television a ranar Lahadi.
Ya ce “Mun samu da kiran waya a game da lamarin da musalin 12:20 Kuma Nan take muka mayar da martani cikin gaggawa da Tattara karfi mu jami’an mu da soja zuwa wajan da abun yafaru.
KARANTA WANNNA LABARIN: Fusatattun Yan Okada Sun Bankawa Wani Gini Wuta A Abuja
“Bayan isowa, sai aka gano cewa an harbi wani mutum, Kuma Nan take aka garzaya zuwa asibiti, inda anan ne aka tabbatar da matuwarsa kuwa ‘ya’yan mata biyu anyi awan gaba dasu”
Nansel ya kara da cewa “Rundunar ta fara farautar wadanda suka aikata wannan aika aika.”
Tuni dai kwamishinan ‘yan sandan ya ziyarci wurin, inda ya jajanta wa wadanda abin ya rutsa da su, ya kuma tabbatar wa da iyalan mamacin cewa za a gudanar da cikakken bincike kuma ba za a bar lamarin ya tafi abanza ba, domin kubutar wadanda aka sace.
A wani labarin Kuma Makamancin wannan.
Fatakwal: ‘Yan Sanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Mutane 31 A Yayin Turmutsutsun Rabon Abinci A Coci
Rundunar ‘yan sandan jihar Ribas ta tabbatar da mutuwar mutane 31 a wani turmutsutsun da ya afku a wani taron coci a Fatakwal, babban birnin jihar a ranar Asabar.
Rundunar ta kuma bayyana cewa wadanda suka samu raunuka “an yi gaggawar kwashe su zuwa asibiti domin jinya cikin gaggawa”.
A cewar sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Grace Iringe Koko, ta ce binciken farko da rundunar ta gudanar ya nuna cewa “abin takaicin ya faru ne a lokacin da mahukuntan Majami’ar suka shirya wani yakin neman zabe wanda ya jawo hankulan jama’a”.
An yi nufin da cewa cocin zata ba da kayan abinci ne ga marasa galihu.
‘Yan sandan sun ce taron ya kasance “ba za a iya shawo kan sa ba” kuma “duk kokarin da masu shirya taron suka yi na ganin sun shawo kan lamarin yaci tura”.
Kwamishinan ‘yan sanda, Friday Eboka, yayin da yake Allah wadai da lamarin, ya umarci mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da ke kula da sashen binciken manyan laifuka na jihar da ya gudanar da bincike na gaskiya kan lamarin.
Ya kuma yi kira ga kungiyoyin addini da na agaji da su tabbatar sun hada kai da ’yan sanda wajen samar da tsaro da kula da jama’a wajen shirye-shiryensu a nan gaba.
Kwamishinan ya kuma jajantawa iyalan wadanda suka mutu tare da yin addu’ar Allah ya jikan su ya kuma basu ikon jure wannan rashi.
Comments 1