JARIDAR DIMOKURADIYYA: Gwamnan Alh. Aminu Bello Masari Ya shedawa Babban Sufeto ‘yan Sandan Nijeriya Muh’d Adamu cewar ‘yan Bindiga sun kwace Wasu Yankuna 8 na kananan hukumomin Jihar.
Da yake Ganawa a madadin Gwamnan Jihar Mataimakinsa’ Alh Mannur Yakubu, ya tabbatarwa Babban Sufeton ‘yan Sandan cewar yanzu haka ‘yan Bindigan a jahar Katsina sune suke Iko da wasu Kauyuka na kananan hukumomin Jibia, Batsari, Safana, da Dan Musa, da Faskari, da Sabuwa, da Kankara, da kuma Dandume.
Haka zalika ya ce akwai wasu kauyika ma da ‘yan ta’addar suka kwace dake yankunan a Mako da ya gabata.