Yan bindiga sun yi garkuwa da Mutane hudu da suka hada da kanwar sirikin Sanata Ahmed Babba Kaita, dan majalisa mai wakiltar Katsina ta Arewa a zauren majalisar dokokin kasar nan.
Daura, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito, yana karkashin Katsina ta Arewa.
Wani mazaunin Kankia, Muhammad Sani, ya ce maharan sun zo ne da sanyin safiyar ranar Litinin inda suka yi ta cin karansu babu babbaka na tsawon wawanni.
Ya ce an kai harin ne a unguwar Bakin Kasuwa, inda suka kai farmaki gidan Mani Babba Kaita, kanin Sanatan, inda suka yi awon gaba da matarsa.
Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun kuma shiga gidan wani Sabe Halilu da ke unguwar inda suka kama matarsa suka yi awon gaba da ‘ya’yansa biyu ciki har da wata ‘yar makarantar firamare.
Wani mazaunin yankin mai suna Salisu Musa ya ce maharan sun kuma yi awon gaba da wata matar aure daga yankin.
“A gaskiya sun zo neman kanin Sanatan ne, amma ya fice daga gidan. Ita ma daya daga cikin matansa ta tsere, amma wanda aka sace, Farida, ta ga ‘ya’yanta suna nan, ba za ta iya barinsu ta gudu ba, ahakan yasa suka kama ta.
“Gaskiya dayar da aka kama, mijinta ba ya gida lokacin da suka zo, don haka yayin da take son tserewa sai suka yi mata dukan tsiya tare da yin garkuwa da biyu daga cikin yaranta. Gaba daya sun yi awon gaba da matan gida biyu da wasu biyu ciki har da wata karamar yarinya,” inji shi.
Kankia muhimmin gari ne da ke kan titin Kano zuwa Katsina. Wannan dai ba shi ne karon farko da ‘yan bindiga suka kai wa garin hari ba.
A wani harin na daban, ‘yan bindiga sun kuma kashe wani direba mai suna Dahiru a kan hanyar Funtua.
Majiyoyi sun ce marigayin ya ki bin ‘yan bindigar a lokacin da suka yi yunkurin yin garkuwa da shi tare da wasu matafiya.
“Marigayi Dahiru ya ki bin su saboda ya ce iyalansa ba su da ikon biyan kudin fansa idan aka yi garkuwa da shi, kuma ‘yan bindigar sun yi barazanar kashe shi a can, sannan ya ce haka ya tabbata daga bsisani,” inji majiyar. .
Kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, bai dauki waya ko amsa sakon wayar ba da aka nemi ya tabbatar da faruwar lamarin har zuwa lokacin hada wannan rahoto.