Hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta Afrika ta Yamma, WAEC ta fitar da sakamakon jarabawar da ta kammala na shekarar 2022 na manyan makarantun sakandare a yammacin Afirka, (WASSCE).
Shugaban ofishin WAEC na kasa, Patrick Areghan ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da yake magana a wani taron manema labarai.
A cewarsa, an fitar da sakamakon ne kwanaki 45 bayan rubuta jabawar darasi na karshe.
Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa an gudanar da jarrabawar na tsawon makonni shida daga ranar 16 ga Mayu zuwa 23 ga Yunin shwkarar 2022.
Chadi ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyoyin ‘yan tawaye
A wani labari kuma na daban.
Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta yi kira ga mahukuntan Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) da su yi watsi da duk jarrabawar da ake yi a makarantar har sai an dakatar da yajin aikin da kungiyar ke yi a fafin kasar nan.
A cewar ASUU, dole ne a sake gudanar da jarrabawar bayan an bi ka’ida.
Jaridar Daily Truat ta ruwaito cewa hukumar gudanarwar makarantar ta sake bude makarantar yayin da KASU-ASUU ta tsaya tsayin daka cewa yajin aikin na ci gaba da gudana a jami’ar
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun kodinetan kungiyar ASUU na shiyyar Kano, Kwamared Abdulkadir Muhammad, ya bayyana cewa idan har mahukuntan hukumar suka gaza soke jarabawar, kungiyar za ta kasance ba ta da wani zabi illa rubuta takardar koke ga hukumar kula jami’o’i ta kasa (NUC) da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC).
“Wadannan jarabawar wasan kwaikwayo da mahukuntan Jami’ar suka ruɗe kuma ake kira da jarabawar da ake yi a KASU a halin yanzu, suna da alaƙa da rashin bin ka’idojin koyarwa, da kuma rashin yi lacca yadda ya kamata
“Rashin halartar malaman da suka koyar da kwasa-kwasan a cikin tsarin tsara tambayoyin jarabawa da sa ido, shigar da dalibai a cikin sa ido da kuma rashin daidaita takardun tambayoyi, wanda hakan ya sabawa ka’idojin da aka gindaya na gudanar da jarrabawar.
“Saboda haka, ASUU ta bukaci a yi watsi da duk wani abin da ake kira jarrabawar da aka gudanar a makarantar ya zuwa yanzu, domin kiyayewa da kuma mutunta tsarin karaty a jami’ar,” in ji shi.