An yi garkuwa da wata basarakiyar gargajiya da mai shekaru 50 da kuma wani matashi a unguwar Otuabula da ke karamar hukumar Ogbia na jihar Bayelsa.
A cewar majiyoyin, ‘yan bindigar da yawansu ya kai 20 ne suka mamaye al’ummar tare da yin awon gaba da mutanen da misalin karfe 1 na safiyar ranar Litinin.
Sun bayyana wadanda aka sace a matsayin mataimakiyar shugaban al’umma yankin, Cif Otia Isomom, Misis Lucy Osain da Mista Friday Abah, wadanda dukkansu aka tsere su a cikin wani jirgin ruwa.
Wani mazaunin garin da lamarin ya faru a gaban idonsa ya ce an daba masa wuka amma ya yi sa’a ya tsere daga sace shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, wanda ya tabbatar da sace mutanen, ya ce ‘yan sanda na kara zage damtse wajen kubutar da wadanda aka sace, yayin da ake ci gaba da bincike domin kama wadanda ake zargi da wannan aika-aika.
A wani labarin Kuma na daban
Zan amince da duk wani hukunci da PDP za ta yanke kan wanda zai tsaya takarar shugaban kasa ——- Gwamna Bala Mohammed
Gwamnan jihar Bauchi kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Bala Mohammed ya bayyana cewa a shirye yake ya amince da matakin da jam’iyyar za ta dauka kan duk wanda zata tsayar domin taka takara zaben shugaban kasa na zaben 2023 mai zuwa.
Bala ya bayyana haka ne jim kadan bayan ganawarsa da wakilan Jaridar Daily Post na jihar Neja a sakatariyar jam’iyyar da ke Minna.
Ya bayyana cewa, hakki na jam’iyya kan lamarin shi ne babba kuma dole ne masu takara su yi biyayya da matakin.
“A matsayina na mai bin dimokradiyya, wannan ba Wani lamari bane na ayi Rai ko a mutu ba. Jam’iyya ce a Samar kowa, kuma dole ne a bi dukkannin matakinta. A shirye nake in bi tsarin shugabanci. Ko da yake, zan gabatar da kaina a gaban dattawan jam’iyyar da ‘yan Najeriya domin su yanke shawarar wanda zai jagorance su anan gaba” in ji dan takarar.
Mohammed ya kuma lura cewa tsarin shiyya-shiyya da ke aiki a PDP ba matsala ba ne, illa dai wata dabara ce ta kawo hanyoyin ruguza mulki kama karya, domin tabbatar da an samu daidaito da adalci a tsakanin al’uma, inda Kuma yace wannan abun ya bawa ne.
“Ni Janar ne a siyasa kuma babu wata matsala idan Mutum Yana da tsarin na guda biyu, saboda koyaushe ina da tsare-tsare ba don kaina ba amma ga mabiyana, daraktocin yakin neman zabe da sauran su,” in ji shi.
Gwamnan ya ci gaba da jaddada cewa “ shiyya-shiyya na cikin kundin tsarin mulkin jam’iyyar wanda da gangan aka yi shi domin tabbatar da zaman lafiya, daidaito da adalci. Dole ne ya zama mambobin da suka yi imani da daukakar jam’iyyar”.