‘Yan bindiga a jihar Neja sun dorawa manoma haraji kafin su girbe amfanin gonakinsu.
A yankin Rumbun Giwa da ke karamar hukumar Mashegu, wata kungiyar ‘yan bindiga, ta umurci duk manoma da su biya wasu takamaimai haraji kafin su cire Amfanin gonakinsu.
Sai dai gwamnatin jihar ta bukaci manoma da al’umma da kada su bi wannan bukata.
Kwamishinan kananan hukumomi, masarautu da tsaron cikin gida, Mista Emmanuel Umar, ya ba manoman tabbacin ba su kariya.
“’Yan bindigar na son manoma su biya wasu kudaden haraji don shiga gonakinsu. Hakan laifi ne kwarai.
“Muna kira ga kowane manomi da kada ya bi wannan umarnin.
“Babu wani manomi da ya isa ya bi wannan umarnin.
“Kada su ba masu don su canza salon rayuwarsu,” in ji shi.
Comments 1