Yan bindiga sun yi garkuwa da akalla Mabiya cocin darikar Living Faith, da a kafi sani da Winner Chapel, dake yanki Osara na karamar hukumar Adavi a jihar Kogi.
A cewar rahoton yan bindiga sun afka cocin ne da yawan gaske, ya yin da Mabiya mambobin cocin ke wani bita a karshen makon daya gabata.
Maharan sun sun fara harbi kan me uwa da wabi a kusa da Majami’ar, domin tsoratar wa kafin daga bisani su yi awangaba da Mambobin cocin zuwa wani wuri da ba’asan ko inane ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hadarin Mota: Mutum 12 sun mutu a hanyar Abuja zuwa Kaduna
Lokacin da ya ke tabbatar da kai harin ga manema labarai, Shugaban karamar hukumar Adavi na jihar Kogi Joseph Omuya Salami, ta bakin Babban Mai bashi shawara akan kafafen yada labarai Habeeb Jamiu ya ce, yan bindigan sun ta yin harbe-harbe a iska domin tsoratar da al’umar yankin, kafin su tafi da wadanda su ka yi garkuwa da su.
A cewar Jamiu, Shugaban karamar hukumar ya ziyarci inda lamarin ya afku, tare da Jami’in dansandan dake kula da yankin na Osara
Kazalika Habeeb Jamiu ya Kara da cewa, Karamar hukumar na tattauna wa da hukumomin tsaron yankin, domin tabbatar da an kubutar da wadanda aka sace lami lafiya.
Sai dai jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Kogi CSP Williams Ovye Aya, bai dauki wayar salula ba kafin hada wannan rahoton.