An yi garkuwa da mambobin wata Coci da ke Akure, babban birnin jihar Ondo a yayin da suke gudanar da Ibada a jiya Laraba.
Wani jariri dan wata shida da limamin cocin na daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a aikin.
Jami’an hukumar Amotekun da ke Ondo sun sanar da cafke daya daga cikin wadanda ake zargi da hannu a lamarin.
Shi dai wanda ake zargin wanda ya yi kama da mace, an kama shi ne a wani daji da ke kusa da wurin bayan ya kutsa kai cikin cocin da ke unguwar Edo Lodge a Akure tare da ‘yan kungiyar sa.
Kwamandan Amotekun a jihar , Adetunji Adeleye, ya ce wanda ake zargin Mai suna Igbekele, an kama shi ne nan take yayin da wasu suka tsere.
Ya ce sun kubutar da mata uku daga hannun masu garkuwa da mutane da suka hada da limamin cocin da jaririyar wata shida.