Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan fashi ne sun yi garkuwa da wani jami’in hukumar tsaron Fararan Hula da Kula da Kaddarorin Gwamnati wato (NSCDC), da wasu mutane hudu a jihar Bayelsa.
Mutanen hudun ma’aikata ne na dan kwangilar dafa abinci na Conoil Producing Limited yayin da jami’in NSCDC na aiki ne da tawagar jami’an tsaro da ke gadin kayayyakin kamfanin mai.
An ruwaito cewa an kai wa wadanda harin ya rutsa da su hari tare da yin garkuwa da su yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa al’ummar Koluama da ke karamar hukumar Ijaw ta Kudancin Ijaw dauke da kayan abinci.
An ce barayin na neman kudin fansa har na naira miliyan 25 domin su sako wadanda lamarin ya rutsa da su, ciki har da matar wani tsohon shugaban tsagerun yankin Fasto Reuben.
Kakakin hukumar NSCDC reshen jihar Bayelsa, Solomon Ogbere, ya tabbatar da sace mutanen.
Ogbere ya ce, “Labari ne tabbatacce. An yi garkuwa da daya daga cikin jami’an mu da wasu fararen hula hudu a ranar Laraba, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wurin da suke kare kayayyakin Kamfanin Conoil.
“Dukkan su suna cikin kayan gida ne yayin da suke komawa sansaninsu lokacin da aka kai musu hari. Ana ci gaba da gudanar da bincike domin zakulo wadanda suka aikata aika-aikar.”