An sace wani malamin jami’ar jihar Kogi, a garin Ayingba, Mai suna Farfesa John Alabi.
An yi garkuwa da shi a jiya Litinin da misalin karfe 6 na yammaci, yayin da wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka afka gidan Malamin
Alabi shine Shugaban Dalibai na Tsangayar Kimiyyar Gudanarwa dake Jami’ar Jihar Kogi.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, masu garkuwa da mutane dauke da muggan makamai sun kutsa cikin Jami’ar ne, da motar kirar Mercedes Benz, sannan suka tafi da shi zuwa inda ba a San ko inane ba.
KARANTA WNANAN LABARIN: Yan sanda sun dakile yunkurin Kungiyar Asiri a Delta, sun kama wadanda ake zargi
Wata majiya daga dangi Malamin ta sanar da wakilin Jaridar Daily Post cewa, masu garkuwar sun tuntubi iyalai da mahukuntan jami’ar jihar Kogi.
Majiyar ta ce, masu garkuwa da mutanen sun kira matar Farfesa Alabi inda suka nemi Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa kafin sakin Malamin.
“Masu garkuwar sun yi wa Farfesa Alabi kwanton bauna da motar Mercedez Benz, lokacin da zai shiga gidansa. Sun so su tafi da shi da motarsa, Amma daga bisani sun tilasta masa ya ajiye motarsa” inji Majiyar.
Kazalika majiyar ta kuma ce,.“Lokacin da suka kira matar Dakta Alabi, sun shaida mata cewa, mijinta yana tare da su. Kuma idan tana son ganin mijinta a raye, to yakamata iyalan su biya naira miliyan ashirin. Hakan ya sa matar ta fara kuka Nan take, saboda dangin ba za su iya samun irin wannan adadin kudaden ba ”