Wasu ‘yan fashi da makami sun kai farmaki a rassan bankunan UBA, Zenith da First Bank da ke Ankpa a jihar Kogi a ranar Talata, inda suka yi awon gaba da wasu kudade da ba a tantance adadin su ba.
‘Yan fashin wadanda adadinsu ya kai 20, an ce sun shigo garin ne da misalin karfe biyu na rana. Da farko sun far wa bankin UBA, kafin su wuce zuwa bankin Zenith daga baya kuma suka afka zuwa FirstBank.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Babu Wanda Zai Iya Saye Na, Bana Kwaɗayin Mukami, Gwamna Wike
Wani ganau ya ce ‘yan fashin sun isa garin ne a cikin motoci da bas da kuma babura.
Shaidun gani da ido sun ce bayan sun yi wa bankuna da ma’aikatan POS da ke kusa da su fashi kusan sa’a guda, ‘yan bindigar sun fita daga garin Ankpa, inda suka rika harbe-harbe.
“Sun yi nisa ta hanyar Okpo, amma babu wanda zai iya fitowa yayin da suke ci gaba da harbe-harbe. Yawancin mazauna Ankpa na nan suna buya,” inji shi.
Ba a dai san ko adadin mutanen da aka kashe ba ya zuwa lokacin da aka fitar da rahoton.
“Ba za mu iya kawar da hasarar rayuka ba. An kai harin sama da sa’a guda,” in ji Ahmed, mazaunin Ankpa.
Wani mazaunin garin ya shaida wa Daily Trust cewa bayan sun tashi ne sai tawagar jami’an tsaro suka taso zuwa yankin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, SP William Aya, bai amsa waya ko sakon waya da aka aike masa ba.
A wani labarin kuma, Tinubu Ya Bayar Da Tallafin Miliyan 50 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Jigawa
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 50 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Jigawa.
Ya sanar da bayar da tallafin ne a lokacin da ya ziyarci Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar a Dutse, a gidan gwamnati.