Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 50 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Jigawa.
Ya sanar da bayar da tallafin ne a lokacin da ya ziyarci Gwamnan Jigawa Muhammad Badaru Abubakar a Dutse, a gidan gwamnati.
KARANTA WANNAN LABARIN: APC Ta Gargadi Shugaban PDP, Kan Wasu Kalamai Ga Wike
Tinubu ya ce: “Na zo nan ne domin in jajanta wa gwamnati da jama’ar Jihar musamman wadanda abin ya shafa da wadanda suka rasa ‘yan uwansu da dukiyoyinsu a sanadiyyar bala’in.”
“Masifar ambaliyar ruwa aiki ne na Allah Madaukakin Sarki. Wannan alama ce kawai don sauƙaƙa wa waɗanda abin ya shafa kar a biya su diyya.”
“Sa’ad da muka ji labarin bala’in da irin barnar da aka yi, mun sa ya zama dole mu zo da kanmu don mu jajanta wa ’yan’uwanmu kuma mu bayyana kanmu kuma mu nuna damuwarmu, haɗin kai da ’yan’uwantaka.”
Da yake mayar da martani, Abubakar ya gode wa dan takarar shugaban kasa bisa wannan ziyara da kuma gudummawar da ya kai masa.
A wani labarin kuma, Najeriya Da Poland Sun Sanya Hannu Kan Wata Yarjejeniyar Fahimtar Juna
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari da takwaransa na kasar Poland, Andrzej Duda, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna kan harkokin noma domin karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannin.
Duda ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a kofar dakin taro na fadar shugaban kasa, dake Abuja jim kadan bayan ganawar sirri da Buhari.