Wasu yan Fashi sun hallaka mutane uku a wani yunkurin fashi da makami da suka yi a wani Banki dake garin Issele-Uku dake karamar hukumar Aniocha ta arewa a Jihar Delta.
Wani shaidar gani da ido ya shaida cewa maharan sun baje abokan aika-aikan su a gurabe da dama inda wasu kuma suka shige bankin ta yadda suka yi ta cin karen su babu babbaka.
Rahotanni sun bayyana cewa abokan huldar bankin da dama sun gaza yin wani katabus inda suka makale cikin bankin yayin da yan bindigar ke ta harbe-harbe a harabar bankin.
“Wannan al’amari abin takaici ne, saboda maharan sun samu nasarar hallaka mutane 4 yayin da wasu da dama suka jikkata, amma nan da nan aka garzaya da su asibiti” a cewar shaidar.
Da aka tuntubi Mai Rikon Muƙamin Kakakin Rundunar Yan Sandar Jihar DSP Bright Edafe ya tabbatar da aukuwar al’amarin to sai dai ya rundunar na ci gaba da tuntubar bangarori daban-daban don jin karin bayani.