Gwamnan Jihar Kano Umar Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa yan fashin daji sun yi sansani a wasu dazukan jihar inda suka maida su maɓoyarsu.
Gwamna Ganduje ya bayyana takamaiman cewa yan bindigar sun fi kamari a dajin Falgore, don haka ne ya nemi agajin jami’an tsaron soji don hana su taka rawar gaban hantsi.
Ganduje ya ce wata kila yan fashin dajin suna wani yunkuri ne na farmakar al’ummar Jihar.
Gwamna Umar Ganduje ya yi wannan batu ne yayin da ya ziyarci Shelkwatar tsaro dake birnin tarayya Abuja a yammacin jiya Alhamis.
“Na kawo wannan ziyara ne don neman agajin rundunar sojin Najeriya don dorewar zaman lafiyar Jihar Kano”
“Yanzu haka yan fashin daji suna can sun yi sansani a dajin Falgore kuma yunkurin kai farmaki ne wa al’ummar Kano” cewar Ganduje.
Da yake maida jawabi, Hafsan Sojin Najeriya Manjo Janar Yahaya baiwa al’ummar kasarnan ne tabbacin cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen maganin duk wani mai mugun nufi wa tsaron kasar.
Ya kuma ce rundunar za ta tashi da kanta zuwa dajin na Falgore don ganin yadda za su far wa al’amari