Daga Sabiu Musa Kano
A wata ziyara da Gwamnan ya kai a laraba fadar Gwamnatin zamfara inda ya yabawa Gwamnan kan yadda yake aiki tukuru Sannan yace a fidda ban-bancin aki’da Ta siyasa a zo a hada kai dan kawo ci gaba a jahar zamfara.
Ya kara da cewa tun can da jahohin biyu aminan juna ne, ya kuma ce ayyukan raya kasa da Gwamnan yake yi abun koyi ne, inda ya Ce tun bayan darewar sa Mulkin jahar abubuwa ke cigaba da dai dai tuwa.
Sannan yayi fatan Allah ya dafa masa kan Wannan abubuwa na alheri da ya tanadawa Zamfarawa da Kasa Baki Daya.
Da yake nasa jawabin Gwamnan jahar zamfara Bello Muhammad matawalle, ya jinjinawa Tambuwal, da tawagar sa da kuma tsohon Gwamnan sakkwato Attahiru Bafarawa, ya kara tabbatar musu da cigaba da hadin kai tsakanin jahohin biyu.
Matawalle, yace zasu ci gaba da aiki Kafada da Kafada da takwaran sa na sakkwato.
Bafarawa, a nasa bangaren ya yaba musu da kuma basu goyon baya da kuma Rokon Allah ya tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.