By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Larabar data gabata ne ‘yan kasuwa a harabar kasuwar Oyingbo dake Legas suka gudanar da zanga-zangar rufe shagunansu.
‘Yan kasuwar da suka yi zanga-zangar a karkashin kungiyar ‘yan kasuwar Oyingbo, suna dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce daban-daban kamar “Folashade Tinubu Ojo ‘yar Ahmed Tinubu, bar kasuwar Oyingbo ita kadai.Karamar hukumar Mainland, ji kukanmu, “Folashade Ojo Tinubu, muna da ‘ya’ya kuma muna karbar hayar gidaje don mu zauna. Mun ƙi zama miyagu”, “Bolla Ahmed, don Allah ka cece mu, ka cece mu daga ‘yarka”, “Don Allah Folashade, ka sake mu daga bautar da muke.”
A cewar ‘yan kasuwar, an rufe rukunin kasuwar ne a makon daya gabata bisa umarnin shugabar kungiyar mata da mazan ta kasuwar sayar da kayayyaki ta Najeriya, Folashade Tinubu-Ojo. bisa zargin baje kolin kayayyaki a cikin wani yanayi mara kyau.